JW subtitle extractor

Rayuwa a Cikin Aljanna

Video Other languages Share text Share link Show times

Ka zauna ka yi tunani cewa
Kana rayuwa a cikin aljanna.
Yara suna wasa.
Ba tashin hankali ko rigima.
Mutanen da suke ƙaunar Allah su ne suke kula da duniyar nan:
“Muddin wata yana nan”—Za mu zauna lafiya da kowa.
Za mu ga ƙaunar Allah da kuma Ɗansa
A cikin aljanna.
Bege na ƙarfafa mu.
Yana sa mu riƙe aminci.
Kamar rana, yana haskawa idan mun ga kanmu
A cikin aljanna.
Ka rufe ido ka yi tunani
Cewa ka gina gida a bakin rafi
Ko a kan duwatsu.
Sai ga wani da ka waye shi,
Yana zuwa gidanka.
Kun gudu kun riƙe junanku, kuma kuna murna.
Domin ya daɗe da kuka ga juna.
Ko mutuwa ma ba ta da iko
A cikin aljanna.
Bege na ƙarfafa mu.
Yana sa mu riƙe aminci.
Kamar rana, yana haskawa idan mun ga kanmu
A cikin aljanna.
Zai cika duk nufinsa.
Za su faru fa, yadda ya ce.
Jehobah zai tabbata, ya cika dukan muradin ’yan Adam.
Bege na ƙarfafa mu.
Yana sa mu riƙe aminci.
Kamar rana, yana haskawa idan mun ga kanmu
A cikin aljanna.